in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta amince da matakan yaki da ambaliyar ruwa a fadin kasar
2018-07-20 23:01:24 cri

Mahukuntan Najeriya sun amince da wasu matakan shawo kan matsalar ambaliyar ruwa dake yiwa wasu sassan kasar barazana.

Gwamnan jihar Anambra dake yankin kudu maso gabashin kasar Willy Obiano ya shaidawa manema labarai jiya Alhamis cewa, majalisar zartarwar kasar ta amince da wasu matakan shawo kan matsalar ambaliyar ruwa, sassauta bala'in da matakan zama cikin shiri, sannan ta kuma gabatarwa ministan muhallin kasar Ibrahim Jibril.

Ya ce majalisar ta kuma amince da kafa sashen tsara ayyuka na tarayya wanda zai kunshi jami'ai daga gwamnatin tarayya, jihohi da PCFRR karkashin shugabancin darekta.

Hukumar samar da agajin jin kai ta jihar Katsina, ta yi rijistar sama da mutane 1,500 da bala'in ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a karamar hukumar Jibia dake jihar. Galibin wadanda bala'in ya shafa mata ne da kanana yara. Haka kuma an tsamo gawawwaki a cikin kogi da gidajen da suka rufta.

A cikin makonnin da suka gabata ne dai, ambaliyar ruwa ta halaka mutane da dama a jihohin Katsina da ogun , inda mutane a kalla mutane 50 suka rasa rayukansu a ranar Litinin din da ta gabata, baya ga gidaje da kadarori da suka salwanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China