
Jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron dandalin tattaunawar harkokin masana'antu da kasuwanci na kasashen BRICS da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. A jawabinsa Shugaba Xi ya ce, duniya na fuskantar manyan canje-canje a halin yanzu, kuma wannan wata kyakkyawar dama da kuma kalubale ne ga kasashe masu tasowa da ma kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa. Ya kamata mu karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS bisa halin da muke ciki, da dukufa wajen raya kasashenmu a lokacin da kasashen duniya ke kokarin bunkasa da kuma ci gaban kasashen BRICS, ta yadda za a kai ga sabon matsayi na samun bunkasuwa cikin shekaru goma masu zuwa. (Maryam)