in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban na kasar Senegal sun yi bayani game da ziyarar shugaban Sin Xi Jinping a kasar
2018-07-22 20:39:34 cri

A ranar 21 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Dakar da nufin fara ziyara a kasar Senegal. Bangarori daban daban na kasar Senegal sun yi bayani game da ziyarar ta shugaba Xi.

Jarida mafi girma ta kasar Senegal "Le Soleil" ta gabatar da bayani na musamman a ranar 20 ga wannan wata, inda aka bayyana yanayin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal a dukkan fannoni. Jaridar ta bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping a wannan karo za ta sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kwalejin Confucius na jami'ar Dakar Mamadou Fall ya bayyana cewa, baya ga bunkasuwar tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ya kamata a koyi kasar Sin a fannin raya al'adu.

Tashar internet mafi girma ta birnin Dakar wato seneweb.com ta wallafa  labarai game da ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Senegal a wannan karo a shafinta na farko. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China