in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana matakan Sin na rage rarar cinikayya a matsayin abun da zai mafanawa tattalin arzikin duniya
2018-05-21 09:18:23 cri

Shugaban cibiyar Peterson, mai nazarin tattalin arzikin duniya, Adam Posen, ya ce kasar Sin ta fara aiwatar da matakan rage rarar cinikayya, wato daidaita kayayyakin da take fitarwa da wadanda ke shiga kasar, tare da sake fasalin tattalin arzikinta, al'amarin da zai yi kyau ga tattalin arzikin duniya.

Adam Posen, ya ce tattalin arzikin kasar Sin ya sauya tsarinsa, inda ya ce kason da ake adanawa ya ragu, sannan wanda ake amfani da shi na karuwa.

Masanin BaAmurke, ya ce idan kasar Sin ta ci gaba da rage adadin kason da take adanawa, matakin zai amfana mata da ma duniya baki daya, abun da zai kara inganta tattalin arzikin duniya.

A cewar Posen, rarar ta kasar Sin na tsakanin kaso 1 zuwa 2 na ma'aunin GDP, wanda adadi ne mai kyau ga kowacce kasa. Ya ce, abu ne da ya bambamta da abun da aka saba gani shekaru 10 zuwa 15 da suka wuce.

Kasar Sin dai ta sake jadadda matsayarta cewa, ba ta neman rarar cinikayya, kuma za ta ci gaba da fadada shigar da kayayyaki kasar, wanda zai ba da sabbin damrmakin ga sauran kasashe su ma su amfana daga kasuwarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China