Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar BRICS, da su yi aiki tare, domin kyautata sabuwar alakar kasa da kasa mai kunshe da martaba juna, da daidaito, da adalci, wanda kuma zai haifar da cimma moriyar juna.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin taron kolin kungiyar BRICS karo na 10 dake gudana a birnin Johannesburg, na Afirka ta kudu, ya ce "ta amfani da rawar da taron ministocin wajen kasashe mambobin BRICS ka iya takawa, da mashawarta a fannin tsaro, da kuma wakilan dindindin na MDD, za mu iya bayyana muryar mu, tare da gabatar da hanyar mu ta warware matsaloli".
Taron kungiyar BRICS na wannan karo dai ya tattara shugabannin kasashe da tattalin arzikinsu ke samun saurin ci gaba, da suka hada da Brazil, da Rasha, da India, da Sin da kuma Afirka ta kudu.(Saminu Alhassan)