in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lamarin samar da allurar rigakafin cuta maras inganci da wani kamfanin kasar Sin ya yi ya jawo hankulan mutane sosai
2018-07-24 20:27:49 cri
A 'yan kwanan nan, batun allurar rigakafin cuta maras inganci ta kamfanin halittu na Changsheng, dake birnin Changchun a lardin Jilin na kasar Sin ya shigar kasuwa, ya yi matukar jawo hankulan mutane.

An gano wannan matsala ne a lokacin da hukumar sa ido kan ingancin magani ta yi bincike kan wannan kamfani. A watan Oktoban shekarar bara, an taba gano cewa, allurar rigakafin cutar Diphtheria da wannan kamfani ya samar ba ta kai ma'aunin da aka tsara ba.

Sabo da haka, wannan ne karo na biyu da aka sake gano laifin da wannan kamfani ya sake aikatawa a cikin rabin shekara da wani abu. Yanzu dai, an riga an nemi kamfanin ya dakatar da aikinsa na samar da magani, sannan gwamnatin kasar Sin ta kafa wani tsarin yin bincike kan lamarin, wato ta tura wani rukunin yin bincike zuwa wannan kamfani domin hanzarta yin bincike kamar yadda ya kamata.

Bugu da kari, hukumar 'yan sandan wurin sun riga sun cafke wasu muhimman jagororin kamfani, ciki har da babbar manajarsa, domin fara binciken su bisa doka. Ya zuwa yanzu, ana hanzarta yin binciken wannan lamari.

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping, wanda har yanzu ke ziyarar aiki a Afirka, ya ba da muhimmin umurni, dake neman a yi bincike ba tare da bata lokaci ba, a kuma tono hakikanin laifuffukan da ke cikin lamarin, kana a yanke hukunci mai tsanani bisa doka kan wadanda suka aikata laifuffukan. Shugaba Xi ya jaddada cewa, dole ne a mai da kiwon lafiyar jama'a a gaban kome a kuma ko yaushe. Kaza lika a kyautata tsarin gudanar da harkokin allurar rigakafin cututtuka, don ba da tabbaci ga babbar moriyar jama'a, da zaman karkon al'umma.

A waje daya firaministan kasar Sin Li Keqiang ya riga ya nemi majalisar gudanarwa, wato gwamnatin kasar Sin, da ta tura wani rukunin yin bincike nan da nan, kan yadda ake samar, da kuma sayar da allurar rigakafin cututtuka gaba daya, domin kokarin gano hakikanin abubuwan da suka haddasa lamarin, kuma a yanke hukunci bisa doka kan wadanda suka aikata wannan laifi ba tare da kau da kai ba.

A 'yan shekarun nan, sau da dama a nan kasar Sin, an kafa ma'aunin samarwa, da kuma yin amfani da allurar rigakafin cututtuka, da tsarin sa ido kan sana'o'in dake shafar allurar. Sakamako hakan, a shekarar 2011 da ta 2014, aikin samarwa, da kuma yin amfani da allurar rigakafin cututtuka da kasar Sin ta yi ya haifar da nasarar samun amincewa daga hukumar WHO har sau biyu.

Amma wannan lamari na samar da allurar rigakafin cututtuka da aka yi, ya sake kawo kalubale sosai ga aikin sa ido kan sana'o'in dake da nasaba da allurar rigakafin cututtuka na kasar Sin.

Bisa shirin da hukumar sa ido kan magunguna ta kasar Sin ta tsara, yanzu haka dole ne dukkan kamfanoni wadanda suke samar da allurar rigakafin cututtuka na kasar Sin, su dauki matakin yin bincike da kansu, domin tabbatar da ganin sun bi ka'idojin da aka tsara, wajen samar da allurar rigakafin cututtuka bisa ma'aunonin kasar, kuma dole ne su samar da cikakkun alkaluman gaskiya masu inganci dake shafar aikin.

Hukumar sa ido kan magunguna ta kasar Sin, za ta yi bincike ne ba tare da sanarwa ba, kafin ma'aikatanta su tashi zuwa dukkan kamfanonin samar da allurar rigakafin cututtuka, sannan za ta yanke hukunci mai tsanani ga kamfanoni ko mutane wadanda suke karya doka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China