in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa Rwanda don ziyarar aiki
2018-07-23 09:24:15 cri

Jiya Lahadi shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa kasar Rwanda a ziyarar aikinsa, wadda ita ce ziyarar aiki ta farko da shugaban na Sin ya kai kasar ta Afrika.

A lokacin isar su, Xi tare da mai dakinsa madam Peng Liyuan, sun samu kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da uwar gidansa madam Jeannette Kagame.

Tun bayan kafa huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu shekaru 47 da suka gabata, Sin da Rwanda suna mutunta juna cikin adalci, da nuna gaskiya, da kyakkaywar alaka.

A tattaunawar da ya gudana cikin annashuwa da Kagame, shugaba Xi ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana gudana cikin yanayi mai tsabta da kuma ci gaba sannu a hankali.

Xi ya ce, a lokacin da mista Kagame ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Sin a watan Maris na shekarar 2017, sun yi tattaunawa mai zurfi game da yadda za'a karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu da kuma yin hadin gwiwa don cin moriyar juna, ya kara da cewa, an samu cikakken aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma matsaya kansu.

Shugaban kasar Sin ya ce, yana sa ran zai yi tattaunawa da Kagame, wanda kuma shi ne shugaban taron kungiyar tarayyar Afrika na wannan karo, game da yadda za'a karfafa dangantaka tsakanin Sin da Rwanda, da Sin da Afrika da kuma sauran batutuwa da suka shafi kasa da kasa da na shiyya shiyya.

Xi ya ce, ya yi amanna cewa, wannan ziyarar za ta haifar da kyakkyawan sakamako wanda zai amfanawa al'ummomin kasashen biyu.

Kagame ya yi maraba da zuwan shugaba Xi a madadin gwamnati da jama'ar kasar Rwanda.

Ya yi imanin cewa, ziyarar ta shugaba Xi a Rwanda za ta kara ingiza hadin gwiwar abokantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China