in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa Afrika ta kudu don fara ziyarar aiki
2018-07-24 09:24:03 cri

Kasar Afrika ta kudu ta shimfida jar darduma domin yin maraba da shugaban kasar Sin Xi Jinping a jiya Litinin a yayin da shugaban ya fara ziyarar aiki a kasar da nufin bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Bayan isarsa kasar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekaru 20 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta kudu ta yi matukar bunkasuwa daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare tsare, wadda ta sauya daga kyakyawar mu'amala zuwa dangantaka bisa matsayin koli.

Kasashen biyu sun fuskanci gagarumin ci gaba na amincewar juna ta fuskar mu'amalar siyasa, da yin hadin gwiwa a aikace, da zurfafa mu'amala tsakanin mutum da mutum, in ji shugaba Xi.

Shugaban na Sin ya ce, yana fatan zai gudanar da musayar ra'ayoyi mai zurfi tare da shugaba Ramaphosa game da batutuwan da suka shafi huldar dake tsakanin kasashen biyu, da batun taron kolin Beijing na dandalin hadin kan Sin da Afrika, da kuma sauran batutuwa da suka shafi kasa da kasa da na shiyya shiyya, da nufin yin hadin gwiwa tare don ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta kudu zuwa wani sabon matsayi na koli a sabon zamani da kuma kawo babbar moriya ga al'ummomin kasashen biyu.

Xi zai kuma halarci taron kolin mambobin kasashen BRICS karo na 10 wanda za'a gudanar a Johannesburg tsakanin ranakun 25 zuwa 27 ga watan nan na Yuli.

Ya kara da cewa, yana fatan zai tattauna game da hadin gwiwa da kuma irin ci gaban da aka samu tare da shugabannin mambobin kasashen BRICS, da kasashen Afrika, da sauran kasashen duniya dake yunkurowa da kuma kasashe masu tasowa, da nufin yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa zuwa wani sabon mataki don bayar da gagarumar gudunmowa wajen ciyar da zaman lafiya da ci gaban duniya gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China