in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hajjn Bana: Buhari Ya Bukaci Alhazan Nijeriya Su Yi Wa Kasa Addu'a
2018-07-24 16:48:58 cri

Mun samu labari daga shafin Intanat na Leadershipayau kan cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga masu shirin tafiya aikin Hajji cewar, su yi wa kasa addu'a saboda samun dorewar zaman lafiya.

Shugaban yayi wannan kira ne ranar Asabar a filin jirgin sama na Nnmadi Azikwe dake Abuja, lokacin da maniyyatan farko daga jihar Kogi, suka fara tashi zuwa Makka,saboda yin aikin Hajja na wanna shekara. Jirgin farko wanda yake dauke da maniyatan jihar Kogi ya tashi ne da misali karfe uku na dare ne.

Ministan babban birnin tarayya Mohammed Bello shi ne wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyanawa maniyyatan cewar, ku yi ma iyalanku addu'a, ku yima kanku addu'a, ku yi ma kasarku addu'a, kuyi ma shugabannin ku addu'a''. Shugaban ya bayyanawa maniyyatan su ci gaba da yi ma kasarsu addu'a, saboda asamu dorewar ci gaba da zaman lafiya.

Ya ja hankalinsu su kasance 'yan kasa nagari da kuma kare addinisu na musulunci.

Bugu da kari kuma ya basu shawarar su yi aiki sannu a hankali, kamar yadda dokoki suka shimfida, su kuma dawo gida lafiya, da ''Hajji Mabrur'' wato (aikin Hajjin da ta karbu).

Muhammadu Buhari ya jinjinawa ita Hukumar aikin Hajji ta kasa akan yadda suke tafiyar da al'amuran aikin Hajji na wannan shekara, ya kara da jaddada cear gwamnatin zata ci gaba da taimaka masu da dukkan abubuan da sukla kamata, saboda su samu damar tafiyar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba maniyyatan Nijeriya shawarar cewar su yi amfamni da damar da Allah ya basu, su tafiyar da aikin Hajji ''Cikin lumana da kuma yadda dokoki suka tanadar''.

Shugaban ya ce, dankon zumunci tsakanin Nijeriya da Saudiyya, zata ci gaba, kamar yadda take tun farko, ya kuma bas u maniyyatan shawarar, '' Su bi dokokin kasar Saudiyya kamar yadda su ke, saboda su ana iya cewa ba yawa gare sub a, idan aka yi la'akari da maniyyatan da zasu zo daga kasashen na duniya''.

Shi ma da yake nashi jawabin shugaban Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa, Abdullahi Muhammed, lokacinn da yake bayanai lokacin da ake kaddamar da fara jigilar maniyyata, 460 wanda jirgin Mad Air ya fara zuwa Madina.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China