in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun dakile wani hari da Boko Haram suka shirya kaiwa jihar Yabe
2018-07-23 09:41:44 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar dakile wani hari da mayakan Boko Haram suka shirya kaiwa wata tawagar sojoji dake sintiri a yankin Sasawa dake jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun sojojin kasa na Najeriya Birgediya-janar Texas Chukwu ya ce, sojojin sun yi nasarar dakile kwanton bautan da mayakan suka shirya kai musu, bayan wani bata kashi inda suka kashe da dama daga cikinsu, kana wasu sojojin sun jikkata, amma kuma al'amura sun daidaita a yankin.

Chukwu ya ce, rahotanni sun nuna cewa, mayakan na Boko Haram sun shirya kai hari tare da kwasar ganima ne a kasuwar Babbangida. Yanzu haka an kara tura sojoji domin kara karfin tawagar sintirin. A halin da ake ciki kuma, mayakan sama na kara yin shawagi ta sama don gano 'yan ta'addan da suka tsere.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China