in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa Abu Dhabi domin ziyarar aiki
2018-07-20 09:55:55 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Abu Dhabi a jiya Alhamis, domin gudanar da ziyarar aiki a hadaddiyar daular Larabawa, ziyarar da za ta zamo irin ta ta farko da wani shugaban kasar Sin zai gudanar a kasar cikin shekaru 29.

Shugaba Xi ya bayyana kasar a matsayin zangon farko na ziyarar sa a ketare, tun bayan sake zaben sa a matsayin shugaban kasar Sin. Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske game da kawance dake tsakanin ta da hadaddiyar daular Larabawa.

Ya kuma kara da cewa, irin kyakkyawar tarba da ya samu daga isar sa masarautar, ta tabbatar masa da irin karfin kawance, da dangantaka dake tsakanin kasar sa da hadaddiyar daular Larabawa, lamarin da ya yi matukar faranta masa rai.

Kaza lika shugaba Xi ya bayyana fatan ci gaba da zurfafa musayar ra'ayoyi bisa manyan tsare tsaren hadin gwiwa, tsakanin shugabanin sassan biyu. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar samun nasarar ziyarar tasa ta wannan karo, da ma burin sassan biyu na karfafa zumuncin dake akwai tsakanin kasashen biyu da ma al'ummun su.

A nasu bangaren, mataimakin shugaban hadaddiyar daular Larabawa, da kuma yariman masarautar, sun yiwa shugaba Xi kyakkyawar tarba, suna masu bayyana shugaban a matsayin dadadden aboki kuma aminin kasar. Sun kuma bayyana zabar kasar a matsayin zangon ziyarar sa na farko tun bayan sake zaben sa shugaban Sin, a matsayin girmamawa ta musamman ga hadaddiyar daular Larabawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China