in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar farko da Xi Jinping zai kai a kasar Senegal na da ma'ana kan ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka
2018-07-20 13:58:45 cri
Bisa gayyatar da shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar daga ran 21 zuwa 22 ga watan. Wannan shi ne karo na farko da shugaba Xi zai kai ziyara kasar dake yammacin Afirka, kuma ziyarar farko da shugaban zai kai bayan da aka sake zabe shi shugaban kasar Sin a watan Maris na bana.

A gabannin ziyarar, jakadan kasar Sin dake Senegal Zhang Xun ya gana da manema labarun kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta zabi kasar Senegal a matsayin zangon farko na ziyarar aiki a Afirka, wannan ya nuna cewa, shugaba Xi da kasarsa sun dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal. Jakadan ya nuna imanin cewa, ziyarar za ta ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba, kana za ta kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China