in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya tattauna da sarkin Abu Dhabi kan dangantakar Sin da UAE
2018-07-22 15:59:24 cri
A ranar Juma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa gayyatar sarkin Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, inda ya halarci fadarsa, shugabannin sun yi musayar ra'ayoyi game da batutuwan da suka shafi karfafa dangantakar kasar Sin da hadaddiyar daular Larabawa da sauran batutuwa dake shafar moriyar bangarorin biyu.

Shugaba Xi ya ce, ta hanyar ziyarar da ya kai a UAE, bangarorin biyu sun yi nasarar cimma sabuwar matsaya, ya kara da cewa, yana da kyakkyawan kwarin gwiwa cewa muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da ingantacciyar makoma.

Shugaban na kasar Sin ya ce, ya kamata kasashen biyu su zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, kana su gina tubalin bunkasuwar alakawar dake tsakaninsu da samar da cigaban bangarorin na dogon zango.

A nasa bangaren, sarki Mohammed bin Zayed ya ce, a shirye hadaddiyar daular Larabawa take ta kasance babbar aminyar kasar Sin mafi girma a yankin gabas ta tsakiya, da kuma yin hadin gwiwa wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da aka cimma matsaya kansu a lokacin ziyarar shugaba Xi, kana da cigaba da karfafa mu'amalar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu daga dukkan fannoni. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China