in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An wallafa kasidar da shugaba Xi ya sanyawa hannu a kafofin watsa labaran Senegal
2018-07-20 22:33:37 cri

A yau ne aka wallafa kasidar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanyawa hannu mai taken "SUNU JAPPO, Sin da Senegal" a jaridar kasar mai suna Le Soleil, gabanin ziyarar aikin da zai kai kasar da ke nahiyar Afirka.

A cikin kasidar, Shugaban Xi ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, kasar Senegal karkashin jagorancin shugaba Macky Sall ta bunkasa, har ma tana alfaharin cimma manufofin raya kasa da aka tsara. Ina Allah-allah na fara ziyara aiki a kasar bisa gayyatar shugaba Sall, wannan wata dama ce ta karfafa alakar fahimtar juna da aboka dake tsakaninmu da zurfafa hadin gwiwa da daga matsayin alakar dake tsakanin Sin da Senegal.

A shekarar 2013, na gabatar da shawarar Ziri daya da hanya daya, hanyar samun bunkasuwa ta bai daya ta hanyar inganta ababan more rayuwar jama'a da hade dabarun raya kasa waje guda. Kasar Senegal da wasu kasashen Afirka da dama sun yi maraba da wannan shawara, inda suka nuna sha'awar shiga a dama da su. A watan Satumban wannan shekara, za a shirya taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) a birnin Beijing na kasar Sin.

Inda za a hade shawarar Ziri daya da hanya daya, da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030 da ajandar raya Afirka ta AU da kasashen Afirka ke fatan cimmawa nan da shekarar 2063 waje guda, taron kolin zai bullo da sabbin damammaki ga alakar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma wata dama ce ta daga matsayin hadin gwiwar Sin da Senagal gaba.

Ya kamata mu karfafa daidaito da mutunta juna.Ya kamata mu kara karfafa dabarunmu na hadin gwiwa. Ya kamata mu zurfafa hadin gwiwa a zahiri. Ya kamata mu karfafa alaka tsakanin al'ummun mu. Ya kamata mu karfafa alaka game da harkokin kasa da kasa da shiyya-shiyya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China