in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Hadaddiyar daular Larabawa zasu bunkasa hadin gwiwar "ziri daya da hanya daya"
2018-07-21 14:41:31 cri
Kasar Sin da hadaddiyar daular Larabawa UAE sun kuduri aniyar bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu karkashin lemar shawarar "ziri daya da hanya daya", kasancewa kasashen biyu sun daukaka yanayin dangantakar dake tsakaninsu zuwa matsayin dangantaka bisa manyan tsare tsare.

Da yake bayani game da daga matsayin dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, a lokacin ziyararsa shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, kasashen biyu suna fatan kafa tsarin cinikayya da zuba jari mai dorewa domin cimma muradunsu.

Game da bunkasuwar harkokin cinikayya dake wanzuwa sannu a hankali tsakaninsu, Sin da UAE sun yi alkawarin kara fadada cinikayya domin cin gajiya a tsakanin kasashen biyu.

Domin kara zurfafa kyakkyawar dangantaka da daga matsayin hadin gwiwar dake tsakaninsu, bangarorin biyu za su gudanar da tarukan kara wa juna sani mai taken "hadin gwiwar gina shawarar ziri daya da hanya daya", kamar yadda takardar bayanai ta tabbatar da hakan.

Kasar Sin tana da dadadden tarihi na yin mu'amala da kasashen Larabawa. A farkon wannan watan, shugaba Xi ya bayyana a wajen taron ministoci na hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa karo na 8 cewa, kasashen Larabawa aminai ne na hakika ga kasasr Sin karkashin hadin gwiwar "ziri daya da hanya daya".

Ministan tattalin arziki na hadaddiyar daular Larabawa UAE, Sultan Bin Saeed Al Mansouri ya bayyana a jiya Jumma'a a lokacin ziyarar kwanaki uku ta shugaba Xi Jinping cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" wata kyauta ce da kasar Sin ta baiwa duniya.

A shekarar 2013 ne, kasar Sin ta gabatar da shawarar mai taken "hanyar siliki ta kan teku da nufin bunkasa tattalin arzikin yankunan dake kan hanyar siliki ta ruwa a karni na 21", da nufin gina tsarin cinikayya da samar da kayayyakin more rayuwa wanda zai hade nahiyar Asiya, Turai, da Afrika a kan dadaddiyar hanyar cinikayyar siliki.

A jawabin da ya gabatar a taron dandalin hadin gwiwar tattalin arzikin Sin da UAE, Al Mansouri ya ce, dangantakar dake tsakanin UAE da Sin tana kara kyautatuwa a 'yan shekarun da suka gabata, kuma za'a daga matsayin danganatakar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa mataki na gaba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China