Wakilin mujallar "Exchange" ta kasar Tanzania Aly Ramji ya bayyana cewa, hukumomin kafofin watsa labaru na kasashen BRICS, sun iya taimakawa kafofin watsa labaru na Afirka wajen raya karfinsu, don gabatar da labarai ta hanyar idon Afirka.
Wakilin kamfanin watsa labaru na "New Times" na kasar Ghana Carol Annang ya bayyana cewa, ya kamata kafofin watsa labaru na Afirka su yi hadin gwiwa tare da na kasashen BRICS, da kara fahimtar juna da yin imani da juna don kafa dandalin watsa labaru na Afirka, da kaucewa daga tsarin sarrafawa na hukumomin wasu kasashen yammacin duniya. (Zainab)