in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsaya game da tsare tsaren hadin gwiwa a dandalin kafofin watsa labarai na kungiyar BRICS
2018-07-20 10:12:22 cri
Mahalarta dandalin watsa labarai na kungiyar BRICS da aka kammala a jiya Alhamis, sun cimma matsaya game da tsare tsaren hadin gwiwa da dandalin zai aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2018 zuwa 2019.

Kafin hakan dai, sai da aka yi doguwar mahawara kan batutuwan da suka shafi ayyuka, da nauyin dake wuyan kafafen watsa labarai, a fannin karfafa tasirin kungiyar ta BRICS. Kaza lika an tattauna game da hanyoyin da suka dace a bi, wajen kyautata hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar, da ma hadin gwiwar kungiyar da nahiyar Afirka.

Kafafen watsa labarai da suka halarci zaman sun yi imanin cewa, duniya na samu ci gaba da sauye sauye, ana kuma aiwatar da gyare gyare a gabar da ake fuskantar yanayi na rashin tabbas, amma duk da haka akwai bukatar ci gaba da kwazo wajen gina al'umma mai makoma guda.

Tsare tsaren da aka amince da su sun kuma kunshi burin kungiyar BRICS, na gudanar da ayyuka a bude, da adalci ga kowa, da karfafa hadin gwiwa, tare da aiki tukuru, domin cimma gajiya ga daukacin bil Adama. Kaza lika tsare tsaren sun kunshi bukatar dake akwai, ta kafofin watsa labaran kasashe mambobin BRICS, su kara kwazo wajen koyi da juna, da musayar kwarewa, tare da fadada musaya ta al'ummu da bayanai, ta yadda za a kai ga cimma nasarorin da aka sanya gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China