Mr. Mataboge ya bayyana kafuwar bankin samar da ci gaba na kungiyar ko NDB a takaice, a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da kungiyar ta cimma.
Jami'in wanda ke jawabi yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki, game da ayyukan kungiyar da ya gudana a jiya Alhamis ya kara da cewa, Afirka ta kudu ta ci gajiyar rance daga bankin wanda ke samar da isassun kudade na gudanar da ayyukan more rayuwar jama'a. Kaza lika a cewar sa, kasar sa na fatan samun karin rance daga bankin a nan gaba.
A nasa tsokacin, wakilin Afirka ta kudun a kungiyar ta BRICS, ambasada Anil Sooklal, ya ce hadin gwiwar kasashe mambobin BRICS na ci gaba da fadada cikin sauri, inda baya ga hadin kai a fannin siyasa, yanzu haka kasashe mambobin kungiyar na zurfafa alakar su ta fannin musaya tsakanin al'ummun su, matakin da zai shafi daukacin sassa na inganta zamantakewar su. Mr. Sooklal ya kara da cewa, dukkanin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS na adawa da duk wani nau'i na nuna wariya da kuma kulla yakin cinikayya. (Saminu)