in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin kafafen yada labarai na BRICS a Cape Town na kasar Afrika ta kudu
2018-07-19 12:24:11 cri

Shugabannin kafafen yada labarai na kasashen mambobin kungiyar BRICS sun gudanar da taro a jiya Laraba domin tattauna batun hadin gwiwa na kafafen yada labarai na mambobin kasashen BRICS, wanda aka bude taron a birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu.

Muhimman batutuwan da taron kolin zai mayar da hankali sun hada da rawar da kafafen yada labarai zasu taka wajen bunkasuwar BRICS, samar da bayanai, da kuma matakan da zasu kara samar da sabuwar hadin gwiwar kafofin yada labarai na mambobin kasashen BRICS.

A sakon maraba ga wakilai mahalarta taron dandalin, mashirya taron sun bayyana cewa, mahalarta taron zasu bada gudunmowa wajen kawo sauye sauye ga ayyukan da kasashen mambobin BRICS ke gudanarwa.

Kimanin kafafen yada labarai 48 daga kasashen BRICS 5 da suka hada da Brazil, Rasha, India, Sin da Afrika ta kudu, da kuma wasu kasashen Afrika da suka hada da Namibia, Zambia da Ghana, ne suke halartar taron a wannan karo.

Kafar yada labarai mai zaman kanta ta Afrika da kudu da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua suka dauki dauyin taron dandalin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China