A ta bakin Henrietta Fore, babban daraktan hukumar UNICEF wanda a farkon wannan shekara ya ziyarci kasar mai fama da yaki, yace a yayin da kasar ta Sudan ta kudu ke cika shekaru 7 da samun 'yancin kai, yakin basasar kasar wanda ba'a san karshensa ba yana cigaba da haifar da mummunar illa ga rayuwar miliyoyin kananan yaran kasar.
Tashe tashen hankula da koma bayan cigaba yana cigaba da ta'azzara a sassan kasar a tsawon lokacin, al'amarin dake barazanar hana yara zuwa makarantu, da fama da rashin abinci mai gina jiki gami da fuskantar cututtuka, bautarwa da kuma cin zarafi.
Yace akwai bukatar bangarorin da basa ga maciji da juna sun rungumi hanyoyin maido da zaman lafiya, Fore ya kara da cewa, "kananan yara a Sudan ta kudu sun cancanci samun kyakkyawar makoma."