in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi gardadi game da girke dakarun kasashen waje a yankin kudancin kasar saboda bakin haure
2018-06-30 16:47:46 cri
Rundunar sojin Libya dake da mazauni a yankin gabashin kasar, ta yi gargadi game da kudurin girke sojojin kasashen waje a yankin kudancin kasar saboda bakin haure.

Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce ta samu bayanan dake cewa wasu bangarori na kasashen waje, na son girke sojoji a wasu yankunan kudancin kasar da sunan magance kwararar bakin haure.

Rundunar sojin karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar, ta ce ta dauki yunkurin a matsayin take dokokin kasa da kasa da kuma kokarin fito-na-fito ga yancin kasar Libya.

Sanarwar ta kara da cewa, rundunar za ta dauki dukkan matakan da suka dace na kare kasar da iyakoki da al'umma da gine-gine da hukumomi da kuma tattalin arzikinta.

Gargadin na zuwa ne, kwanaki kalilan bayan mataimakin Firaministan Italiya Matteo Salvini, ya gabatarwa Gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya, bukatar kafa cibiyoyin karbar bakin haure a kudancin Libya, bukatar da Gwamnatin kasar ta ce ta ki amincewa da ita. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China