in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta bukaci MDD da ta haramta sayar da danyen mai ta haramtacciyar hanya
2018-06-27 10:01:11 cri
Gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD ta bukaci kwamitin sulhu na MDDr da ya dakile duk wata hanyar da 'yan adawarta dake gabashin kasar take bi wajen sayar da albarkatun man kasar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da dakarun sojin dake gabashin kasar suka ayyana a ranar Litinin cewa zasu damka yankin nan mai arzikin mai ga gwamnatin dake gabashin kasar.

Gwamnatin mai samun goyon bayan MDDr ta yi Allah wadai da sanarwar, wadda ta bayyana cewa wasu haramtattun jam'iyyu ne ke yunkurin damka tashar albarkatun man kasar ga haramtacciyar gwamnatin da ba'a amince da ita ba.

Sanarwar tace, wannan yunkuri ya sabawa tsarin shugabanci da kuma ka'idojojin hukumar kula da albarkatun man kasar, ta kara da cewa, hukumar kula da albarkatun mai dake zaune a Tripoli ce kadai halastaciyyar hukumar kula da albarkatun mai ta kasar, kuma itace kadai ke da alhakin tafiyar da harkokin tashar samar da man kasar da kayayyakin ayyukan samar da man.

A cewar sanarwar wannan yunkurin zai kara haifar da rarrabuwar kai da mayar da hannun agogo baya game da yunkurin da ake yi a cikin gida da matakai na kasa da kasa na samar da dawwamamman zaman lafiyar kasar.

Gwamnatin ta bukaci kwamitin sulhun MDDr da kwamitin ladaftarwa da su bincika tare da dakatar da duk wani mataki na sayar da man kasar ta haramtacciyar hanya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China