in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan karfafa hadin kan kasa da kasa da bangarori daban daban wajen aiwatar da dokoki
2018-07-03 20:31:09 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Talata cewa, sanarwar shugaba da aka bayar a yayin taron dandalin tattaunawar hadin kai kan aiwatar da dokoki tsakanin kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da aka shirya a kwanan baya a nan birnin Beijing, ta bayyana cewa, ya kamata a hada kai don aiwatar da dokoki bisa tushen yin shawarwari tare, da raya wa, da kuma samun moriya tare, kana da sa himma wajen rigakafi da kawar da cacar baki yadda ya kamata, da nufin nuna goyon baya ga shawarar "Ziri daya da hanya daya" a fannin dokoki, da ba da tabbaci kan batun a fannin tsare-tsare.

Baya ga haka, Lu ya nuna cewa, kasar Sin na fatan karfafa hadin kai tare da bangarori daban daban a dukkan fannoni, ciki har da aiwatar da harkoki bisa dokoki, don ciyar da aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" gaba.

An shirya taron dandalin tattaunawar hadin kai kan aiwatar da dokokin kasa da kasa ne jiya Litinin zuwa yau Talata a nan birnin Beijing. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China