in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawar hadin kan aiwatar da dokoki tsakanin kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya"
2018-07-02 20:13:48 cri
Yau Litinin, aka bude taron dandalin tattaunawar hadin kan gudanar da dokoki na kasa da kasa a nan birnin Beijing, wanda ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, da kungiyar lauyoyin kasar suka shirya

A jawabinsa yayin bikin bude taron, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya nuna cewa, aikin tafiyar da harkoki bisa doka, shi ne zai yayata shawarar "Ziri daya da hanya daya" zuwa sauran sassan duniya, shi ne kuma muhimmin abu wajen tinkarar duk wani hadari.

Baya ga inganta hadin kai wajen raya manyan kayayyakin more rayuwa game da shawarar, akwai bukatar su karfafa hadin kansu a fannin dokoki da ma'auni game da shawarar, kana su kara kyautata tsarin ba da tabbaci ga shawarar a fannin gudanar da dokoki bisa doka, da zurfafa yin cudanya da hadin kai tsakanin kasa da kasa a fannin. Baya ga haka, kasar Sin za ta samar da kudin tafiyar da ayyukan nazarin hadin kan gudanar da dokoki bisa doka game da shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin nuna goyon baya ga kasashen da shawarar ke shafa wajen kara karfinsu na tafiyar da dokoki, da horar da kwararru a fannin dokokin kasa da kasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China