in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shigo da tunanin raya duniya ta bai daya cikin takardar sakamakon taron MDD kan sararin samaniya
2018-06-21 15:10:18 cri

An kira taron tunawa da cika shekaru 50 da MDD ta yi bincike da amfani da sararin samaniya cikin lumana a jiya 20 ga wata a birnin Vienna. Takardar sakamakon da majalisar ta samu da aka zartas da ita a wannan rana ta shigo da tunanin da Sin ta gabatar, wato yin kira da a kara hadin kai wajen yin amfani da sararin samaniya, ta yadda za a raya duniyar bai daya da kawo moriya ga dukkanin bil adama.

Wannan takardar da aka shirya har tsawo shekaru 3 tare da tattaunawa a kanta sau da dama, daga baya dai ta samu matsaya daya daga dukkan mambobin MDD, wadda za a gabatar da ita ga babban taron majalisar karo na 73 don a zartas da ita. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China