Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ambaci yadda za a kara kyautata huldar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da tsare-tsare masu alaka da hadin gwiwarsu, da matakan da za a dauka don kyautata fasalin dandalin hadin gwiwar. Ban da haka kuma, shugaban ya bada shawarwari game da yadda kasar Sin da kasashen Larabawa za su kara hada kai wajen aiwatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya", gami da bayyana shawarar kasar Sin kan wasu matsalolin da ake fuskanta a yankin gabas ta tsakiya, don neman biyan bukatun bangarori daban daban masu ruwa da tsaki. (Bello Wang)