A ganin masanan kasar Sin, kara harajin kwastam da Amurka ta yi, ra'ayi ne na kama karya kan ciniki, kuma kasar Sin ta yi imanin tattalin arzikinta zai bunkasa yadda ya kamata.
Daga cikin jerin kayayyakin Sin da Amurka ta karawa harajin kwastam da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 34, kamfanonin kasashen waje, kuma galibinsu kamfanonin jarin kasar Amurka ne dake nan kasar Sin ke samar da wadanda darajarsu ta kai fiye da dalar Amurka biliyan 20, wanda ya kai kashi 59 cikin dari bisa na jimilar kayayyakin. Game da wannan, babban manazarci na cibiyar nazarin tattalin arziki da yin mu'amala ta kasar Sin, Zhang Yansheng, na ganin cewa, Amurka na son yin amfani da yakin ciniki don tilastawa kamfanonin kasarta komawa gida, wanda aiki ne na koma baya ga tsarin raya duniya baki daya, da ba zai cimma nasara ba.
A nasa nazarin, mataimakin shugaban kwalejin nazarin tattalin arziki bisa manyan fannoni na kasar Sin Bi Jiyao ya ce, kara harajin kwastam kan kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 34, ba zai yi tasiri mai yawa kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa ketare da bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci mai zuwa ba. (Zainab Zhang)