in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar ya hana a zuba mata jari
2018-07-10 10:44:11 cri
Wani rahoton da kamfani mai nazarin tattalin arziki na Rhodium Group na kasar Amurka ya bayar a kwanakin baya ya nuna cewa, tun daga watan Janairu zuwa na Mayun bana, kasar Sin ta zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 1.8 ga kasar Amurka, wanda ya ragu da kashi 92% idan an kwatanta da jamillar makamancin lokacin bara. Bisa wannan lamarin, Wang Huiyao, babban darektan cibiyar nazarin al'amuran tattalin arziki na CCG na kasar Sin, ya yi tsokaci cewa, yadda kasar Amurka ta tayar da yakin ciniki ya sanyaya gwiwar kamfanonin kasar Sin wajen zuba jari ga kasar Amurka. Lamarin, a ganin Wang, tamkar yadda kasar Amurka ta yi watsi da dimbin guraben aikin yi, ta kuma mika su ga sauran kasashe.

Wang ya kara da cewa, a shekarun baya kamfanonin kasar Sin sun yi kokarin zuba jari ga kasuwannin Amurka. Misali, kamfanin samar da gilashin motoci na Fuyao ya zuba dalar Amurka biliyan 1 don bude wasu ma'aikatu a kasar Amurka, inda aka samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai dubu 3 zuwa dubu 4 a can. Sai dai a halin yanzu, a cewar mista Wang, yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar da shi ya tilastawa kamfanonin kasar Sin yin watsi da aniyarsu na cigaba da zuba jari a kasar Amurkar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China