in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da wani shirin samar da aikin yi na musamman ga baki 'yan kasashen waje dake Sin
2018-07-09 09:59:27 cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, an kaddamar da wani shiri na kasa da kasa da nufin samar da guraben ayyukan yi na musamman ga baki 'yan kasashen waje.

Manufar shirin wanda dandalin dake karin haske kan guraben ayyukan yi na kasa da kasa na LinkedIn da " I'm in China" suka kaddamar, ita ce yayata al'adu da tarihin Sinawa.

Guraben ayyukan yin da ake fatan baki 'yan kasashen waje za su samu, sun hada da bangaren wasan Kung fu a wurin Ibadar Shaolin, aikin kula da dabbar Panda, ma'aikacin kula da jirgin kasa mai saurin tafiya, aikin kwashe shara a gandun dajin Zhangjiajie da mai rikon mukamin shugaban cibiyar Yuelu da mai dafa taliya da naman sa, direban babbar mota a kan tagwayen hanyar Qianhai-Tibet da masani kan cinikayya ta yanar gizo.

Baki 'yan kasashen waje miliyan 520 dake amfani da shafin Linkedln na iya rjiistar neman wadannan guraben ayyukan na watanni shida.

Yanzu haka ana kara samun baki 'yan kasashen waje dake zuwa kasar Sin domin inganta rayuwarsa, biyo bayan ci gaban tattalin arzikin kasar dake kara samar da tarin damammaki.

Wani rahoto da shafin na Linkedln ya fitar a kwanakin baya ya nuna cewa, biranen Beijing da Shanghai da Shenzhen da Guangzhou da Hangzhou sun kasance birane biyar dake sahun gaba wadanda ke kara daukar hankalin bakin 'yan kasashen waje masu mu'amula da wannan shafi (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China