Nahiyar, karkashin shugabancin hukumar ta ECA, ta samu gagarumin ci gaba bisa gudunmowa da kuma irin jajurcewar da marigayi Adedeji ya nuna ta hanyar shirya taruka da tattaunawar da ya jagoranta lokacin ya rike da ragamar shugabancin hukumar, an yi bikin binne shi a ranar Juma'a a kasarsa ta haihuwa Najeriya.
Daruruwan shugabannin tsare tsare na Afrika da kwararru cikinsu har da shugabannin wasu kasashen Afrika da suka hada da shugaban kasar Namibia Hage Geingob, da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, da tsahon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da kuma manyan jami'an hukumar ECA ne suka bayyana jinjinarsu bisa ga irin nasarorin da Adedeji ya samar ga ci gaban Afrika, kamar yadda hukumar MDDr ta sanar a jiya Asabar.
Adedeji, wanda ya shugabanci hukumar ECA na tsawon shekaru 16 daga shekarar 1975 zuwa 1991, an bayyana jami'in a matsayin wani babban jigo kuma jagoran tabbatar da cigaban nahiyar Afrika a karni na 20. (Ahmad Fagam)