in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Annobar Kwalara: Akwai Bukatar Al'umma Su Yi Wa Kawunansu Rigakafi
2018-07-04 10:12:24 cri
Mun samu wannan labari daga shafin Internet na "Leadership a Yau".

Yanzu a kasar Najeriya Damina ta shigo kuma cutar kwalara ta kunno kai. A rahoton da cibiyar shawo kan cututttuka ta kasa ta wallafa (NCDC), ta sanar da cewar, a cikin sati daya da ya gabata kacal, an samu bullar annobar har guda 832 da ake zargi a yankuna sha shida dake cikin jahohi shida. An kuma tabbatar da bullar annobar guda takwas, inda kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane takwas. Adadin a bayan satin ya kuma karu zuwa yawan 190 a cikin yankuna sha daya dake cikin jahohi bakwai, inda aka tabbatar da mutane sha bakwai sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane sha bakwai.

A shekarar data wuce kuwa, an samu bullar annobar guda uku da ake zargi a karamar hukumar Kaduna ta Kudu. A kalla an ruwaito bullar annobar har guda 5,659 da ake zargi tun a cikin watan Janairu, inda a jimlace rahotanni suka ce, annobar tazo ne daga kananan hukumomi sittin da daya dake cikin jahohi sha tara kuma daga cikin wannan adadin guda 162 anyi masu gwajin sun kamu da annobar kuma mutane tamanin da hudu suka rasu.

Har ila yau, a shekarar data gabata mutane hudsu suka mutu daga cikin mutane tamanin da biyar da ake zargin sun kamu da cutar a jahohi sha daya. Barkwar cutar ta kwanan ta bulla ne a jahohin Adamawa da Bauchi da Borno da Zamfara da Kaduna da Kano, sai kuma birnin tarayyar Abuja, inda ta kai guda dari a jihar Adamawa sai Abuja da Zamfara suna da kashi daya. Adadin yana kara karuwa, inda yake kara yada cutar sakamakon watsar da ledoji da rashin kwashe bola da yin bahaya ako ina barkatai. Dukkan hukumomin NCDC da WHO sun bayar da gargadi akan yaduwar annobar a daminar bana tare da sanar dabarun da za a dauka don kare kai daga annobar.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta yi gargadin cewar, annobar zata fi watsu a cikin daminar bana in har ba'a dauki matakan magancewar a cikin gaggawa ba. A cewar jami'an bayar da agajin gaggawa na sashen kiwon lafiya na WHO Ifeanyi Okodu wannan ba abune boyayye ba domin bayanan da aka samu a shekarun da suka wuce sun nuna cewar, a bisa tarihi cutar tafi tsananta a lokacin da aka fara damina. A cewar sa, kasancewar sanin wannan ilimin, yana taimakawa wajen yin hadaka don gudanar da shirin kota kwana da shirin samar da kayan kiwon lafya da horas da jami'an kiwon lafiya don sanya ido wajen kai dauki idan annobar ta bulla.

A cewar Adeolu Alakija, wanda ya taron tattunawa a yankin Arewa maso gabas akan annobar ya sanar da cewar, a shekarar data gabata jihar Borno ta fuskanci barkewar annobar, amma masana sunyi amannar akan cewar annobar ta dauki darasi akan yadda zata magance annobar,inda ya kara da cewar, maganar cutar bawai kawai maganar magani bane abune da ya shafi ruwa da kuma yin rigakafi. Ya kara da cewar, a shekarar data gabata anyi kokari wajen yiwa mutane su 915,000 allurar rigakafin cutar, a wanannan shekarar kuwa mun yi kokarin dakile cutar a matakin farko. An dauki matakan gaggawa so sai don dakile yaduwar cutar, inda majalisar dinkin duniya ta amince da naira miliyan 720 ta hanyar bayar da agaji ta gidauniyar bayar da dauki ta Nijeriya don dakile yauwar cutar a jihar Yobe.

Kungoyoyi kamar Medecins Sans Frontieres, wadda ita ce ta farko data kawo rahoton barkewar annobar ta tainaka wajen kafa cibiyoyi warkar da wadanda suka kamu da cutar, sannan kuma daga baya an kara mayar da hankali wajen fadada gano yaduwar cutar da kuma gano wadanda suka kamu da cutar. Daya dabarar da aka dauka kuma ita ce, hanyar ruwa da cutar ka iya yaduwa har a kamu da ita, kuma kamuwa da cutar ya danganta ne da irin rayuwar da alumomi suke gudanarwa. Mutane da dama da suka kamu da kwayoyin cutar, bata nuna masu wasu alamomi, amma kwayoyin suna kasancewa a fuskokin su har zuwa kwanuka goma sai kuma suyi ba hayar kwayoyin a fili, wannan wuri ne da ruwa ke wwuce wa.

A cewar Ngozi Azodoh, darakta ta aiki na musamman a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya, an kai dauki da ya kai a kalla ashirin da biyar da ban-da-ban a jahar Borno don a dakile barkewar cutar. Har ila yau, a cewar darasin da aka koya a shekarar data wuce na barkewar cutar Red Mpazanje, wanda ya wakilci daraktan WHO a Nijeriya Wondi Alemu a lokacin taron tattananawa Abuja akan yankin arewa maso gabas cutar ta kashe kimanin mutane 143,000 a duniya. Ya yi nuni da cewar goma a cikin shida na wadanda suka mutu ta auku ne a nahiyar Afrika sakamakon rashin daukar matakan gaggawa.

A bisa bayanan da masu bincike suka karbo, ya nuna cewar barkewar cutar a nahiyar Afrika talatin da bakwai daga shekarar 2010 zuwa 2016. Sakamakon daminar jahohi sha takwas suna fama da cutar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China