Da yake jawabi a taron koli game da al'amurran tsaro a jahar Imo dake kudancin kasar, Idris ya ce kamata ya yi al'ummomin yankunan kasar su hada kai da jami'an 'pyan sandan wajen gano bata gari domin dakile ayyukan bata garin.
Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin al'ummomi da 'yan sanda, ya ce jami'an 'yan sandan ba za su iya kawo karshen matsalolin tsaro dake zama barazana a kasar ba tare da samun goyon bayan jama'a ba.
Idris ya fadawa mahalarta taron cewa, 'yan sanda suna bukatar hanyoyin sadarwa, da fasahohin sadarwa na zamani, da na'urorin gudanar da bincike na zamani wadanda za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukan bincike.
Sifeton ya bukaci 'yan kasar da su yabawa kokarin da jami'an 'yan sandan kasar ke yi bisa irin nasarorin da suka cimma kawo yanzu game da yaki da bata gari a fadin kasar.
Jami'in ya buga misali da irin nasarorin da 'yan sandan Najeriyar suka samu na baya bayan nan musamman a yankin kudu maso gabashin kasar wadanda suka hada da damke shahararren mai yin garkuwar da mutanen nan da aka fi sani da Vampire da kuma kama wani shahararen mai garkuwa da mutanen mai suna Evans. (Ahmad Fagam)