Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar jiya, ta ruwaito Sakatare Janar din na maraba da matakan da aka dauka na warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu.
A wannan watan ne, Ethiopia ta sanar da shirinta na amincewa da kuma aiwatar da yarjejeniyar kan iyaka ta 2002, da ta kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru 2 ana yi tsakanin kasashen, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane. Idan babu yarjejeniyar, za a ci gaba da gwabza fada, inda ake zargin Eritrea da kasancewa cikin shirin yaki.
A wani jawabi da ya yi a wannan makon, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki, ya sanar da shirinsa na tura wakilai zuwa Addis Ababa, domin nazarin halin da ake ciki da kuma tattaunawa kai tsaye tare da tsara matakan da za a dauka a nan gaba. (Fa'iza Mustapha)