Shugaban kasar Eritrea ya gana da tawagar sada zumunta ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin
Kwanan baya shugaban kasar Eritrea Isaias Afewerki, ya gana da tawagar sada zumunta ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Asmara, wadda ke karkashin jagorancin wani babban jami'in jam'iyyar mai suna Cui Shaopeng. Isaias ya bayyana fatansa na inganta hadin-gwiwa tare da kasar Sin, domin kara yin mu'amala a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
A nasa bangaren, Cui Shaopeng ya isar da sakon gaisuwa na shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa ga Isaias, ya kuma ce, kasar Sin na son kara yin cudanya da hadin-gwiwa tare da jam'iyyar PFDJ mai mulkin kasar Eritrea, a wani kokari na ci gaba da raya hulda tsakanin kasashen biyu.(Murtala Zhang)