Abdelkader Messahel ya bayyana haka ne yayin bude wani taron yanki karo na 3, kan kare kaifin kishin addini da ya gudana a Algiers, babban birnin kasar.
Ya kuma ce manufar taron ita ce, musayar kyawawan ayyuka da gogewa, wanda Algeria ke da su a matakai daban-daban.
Ministan ya ce babbar manufar irin taron ita ce, tattara kokarin kasashe daban-daban tare da karfafa kwarewarsu na yaki da barzanar da bata da iyaka.
Har ila yau, ya ce kafofin sadarwa na zamani da rashin kudi tsakanin matasa ne ke taimakawa yaduwar tsattsauran ra'ayi da kaifin kishin addini a wasu sassan Afrika. (Fa'iza Mustapha)