in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Baki masu bada horo na kokarin cika burin yaran kasar Sin na zuwa gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya
2018-07-04 14:52:56 cri

A yayin da guguwar gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ke kadawa a duniya, masoya kwallon kafa sun zabura, inda suke cike da dimbin buri. Matasa da masu bada horo na kasar Sin ma ba a bar su baya ba, inda suke da yakinin cewa, nan gaba kadan, kasar Sin za ta shiga a dama da ita cikin harkar wasannin kwallon kafa a duniya.

Dangane da wannan batu ne Wakiliyarmu Fa'iza Muhammad Mustapha ta hada mana rahoto, inda ta duba yanayin da wasu ayarin matasa Sinawa da baki masu horas da su ke ciki a lardin Guizhou na kasar Sin mai albarkar tsaunuka.

"Kara gudu!" "mika kwallon!" "Buga!" "da kyau!"… Kalaman masu bada horon ke nan yayin da matasa ke gudu da buga kwallo cike da annashuwa da jajircewa a filin wasa na makarantar kwallon kafa ta Zhenhua dake birnin Kaili na yankin Qiandongnan na kabilun Miao da Dong mai cin gashin kansa.

Masu horon sun hada da Jose Hernandez Suarez dan kasar Spaniya da mataimakinsa dan kasar Chile, Mauricio Javier Martinez Neira.

Jose Hernandez mai shekaru 48 ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan ne karo na 3 da shi da Martinez suke bada horo kyauta ga daliban.

Ya yi bayanin cewa, su kan tsara shirye-shiryen koyarwa bisa la'akari da shekarun daliban, inda ya ce sun samu kwarin gwiwar bada horon ne daga tsarin horar da kwallon kafa na Spaniya, wanda ke koyar da nagarta da sanin ya kamata.

A cewar Jose Hernandez, horon ya kunshi wasannin motsa jiki na zaburarwa da fasahohi da dabaru daban-daban da ake bukata da kuma wasanni tsakanin kungiyoyi.

Mai bada horon ya ce babu wani bambanci mai yawa tsakanin matasan kasar Sin da na Turai. Yana mai cewa, duk da cewa matsakaicin tsawon daliban kasar Sin ya yi gajarta, burinsu na son koyo da kokarinsu na ganin sun samu nasara na da karfi, kamar na sauran 'yan wasan duniya.

Ya kara da cewa, karin bambancin dake akwai shi ne, gwamnati na tallafawa matasa 'yan wasa, wanda ba safai ake gani a Turai ba.

A cewar kwararren mai bada horon, har yanzu, kungiyoyin yankuna a kasar Sin na da damar kara fadada, yana mai cewa, akwai kungiyoyin yankuna a galibin biranen Turai, har ma a makarantu, inda yara kan yi atisaye tare da gasa a tsakaninsu domin ci gaba da bunkasa kwarewarsu.

Ya ce ba kamar Turai ba, wannan na gudana ne sau daya cikin watanni 2 ko 3 a birnin Kaili. Tsohon kwararren dan wasan kwallon kafar wanda daga bisani ya zama mai bada horo, ya shafe shekaru 20 yana horar da kungiyoyin yara a Spaniya.

Kafin zuwansa Kaili, Jose Hernandez, ya yi shekaru 2 yana bada horo a Chengdu, babban birnin lardin Sichuan, daga bisani kuma ya koma Kaili saboda yanayin wasan kwallon kafar garin da ya burge shi.

Bayan isarsa Kaili, ya rattaba hannu kan kwanturagin shekaru 2 da kungiyar Guizhou Fengyun, dake horar da matasa masu hazaka.

Ya ce falsafarsu ita ce, ta hanyar mayar da hankali ga horar da matasa, za su iya samun nasara a nan gaba. Inda ya ce yana sane cewa hanyar na da tsawo, domin za ta bukaci aiki na shekaru 10 zuwa 20.

Mauricio Martinez mai shekaru 24, wanda mataimaki ne kuma aboki ga Jose Hernandez, ya kasance mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta kasar Chile, inda a shekarar 2014, ya tafi Chengdu domin aiki a matsayin mai bada horo ga kungiyar yankin. A bana ne kuma ya dauki shawarar abokinsa Hernandez, inda ya dawowa kasar Sin domin taimaka masa horar da matasan Kaili masu basira.

Matashin ya jadadda cewa, a ganinsa, koyar da matasan kasar Sin dukkan abun da ya sani game da kwallon kafa, kyakkyawar dama ce gare shi.

Mauricio Martinez, ya ji dadin ganin yadda yara a Kaili ke cike da buri da son yin gasa. A cewarsa, ci gaba da kara kokarin kan inganta dabarunsu, shi ne abun da suke bukata.

Ya kuma bayyana yakininsa kan harkar wasannin kasar Sin. Yana mai cewa, kasar Sin na da dimbin damammaki a fagen kwallon kafa, kuma abun da kawai ake bukata shi ne bunkasa harkar. Ya ce cikin shekaru kalilan, kasar za ta zama mai karfi a harkar kwallon kafa.

Sai dai kuma rayuwa a Kaili na yi wa masu bada horon wuya. Misali, baya ga Martinez da mai fasara na kungiyar, Jose Hernandez ba shi da wanda zai iya yi wa magana da harshensa na asali.

Ga Mauricio Martinez tsohon dan wasan na kasar Chile, babbar matsalarsa ita ce, har yanzu bai saba da abinci mai yaji da mutanen yankin suka fi so ba. Baya ga haka, yana kewar 'yarsa mai shekaru 2 dake Chile.

Abu daya da masu horon ke fata shi ne, dauko iyalansu su zauna tare da su, sannan su shaida da damawa cikin ci gaban harkar wasanni a kasar Sin.

Mafarkinsu na kokarin zama gaskiya, inda a yanzu ake bada horo kan kwasa-kwasan kwallon kafa kyauta a makarantun firamare da sakandare a birnin Kaili, wanda ya samo asali daga shirye-shiryen kungiyar kwallon kafa ta Fengyun da hadin gwiwar gwamnatin yankin.

A cewar shugaban Kungiyar Fengyun, Yao Yu, suna shirin kara wasu masu bada horo biyu 'yan kasar waje domin fadada ayyukansu na bada horo da kuma bada horo akai-akai ga dalibai.

Shugaban kungiyar na da yakinin cewa, idan aka ci gaba da irin wannan tsarin bada horon, wata rana kungiyar kasar Sin za ta koma kasar kwallon kafa ta cin kofin duniya. Idan kuma hakan ya faru, burinsa daga cikin 'yan wasan, a samu wadanda Hernandez da Martinez suka horar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China