in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu na goyon bayan burin Morocco na karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a 2026
2018-04-17 21:11:58 cri

Hukumar gudanarwar kwallon kafa ta Afirka ta kudu SAFA, ta bayyana goyon bayan ta ga burin kasar Morocco, na neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2026.

Wata sanarwa da shugaban hukumar ta SAFA Danny Jordaan ya sanyawa hannu, ta ce Afirka ta kudu na marawa Morocco dake arewacin nahiyar Afirka baya bisa wannan kuduri.

Sanarwar ta biyo bayan zantawa tsakanin Mr. Jordaan da tawagar wakilan kasar Morocco, wadda aka dorawa nauyin tallata manufar kasar ta karbar bakuncin gasar ta duniya da hukumar FIFA ke shiryawa.

Tawagar ta Morocco dai ta kunshi wakilin kasar, tsohon dan wasan kasar, kuma tsohon dan wasan Liverpool El Hadji Diouf, da kuma tsohon mai tsaron gidan kasar Kamaru Joseph-Antoine Bell.

Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Jordaan ya ce bukatar kasar Morocco bukata ce na nahiyar Afirka, don haka ya ce shi da kan sa zai nemawa Morocco goyon baya a hukumar COSAFA da ma sauran yankunan nahiyar Afirka baki daya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China