in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta fitar da sunayen 'yan wasan wucin gadi 30 da za su je gasar cin kofin duniya a Rasha
2018-05-15 09:19:44 cri
Kocin tawagar kwallon kafa ta Najeriya Gernit Rohr ya sanar da sunayen 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za a yi kasar Rasha.

'Yan wasan sun hada da Junior Lokosa da Simeon Nwanko, da Leon Balogun, da Wilfred Ndidi, da Etebo Oghenekaro, da Jeol Obi da Trone Ebuehi.

Yanzu haka dai an shirya 'yan wasan za su yi wasan sada zumunta da Jamhuriyar demokiradiyar Congo a ranar 28 ga watan Mayu da muke ciki, kafin su isa London inda za su fafata da Three Lions a filin wasa na Wembley a ranar 2 ga watan Yuni kafin daga bisani su fafata da Jamhuriyar Czech a ranar 6 ga watan Yuni.

Najeriya dai na rukuni na 4 hudu a gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Rasha, tare da kasashen Argentina da Iceland da kuma Croatia. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China