A lokacin da yake karba bakuncin tawagar 'yan wasan a Abuja fadar mulkin kasar, shugaban Buhari, ya kuma bukaci 'yan wasan dasu gudanar da ingantaccen wasa mai tsabta a wasan cin kofin duniyar.
Tawagar 'yan wasan ta Super Eagles zata yada zango ne a Ingila a ranar Laraba da zarar ta kammala ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasar a gaban wasu daga cikin mambobin majalisar zartaswar kasar da jami'an hukumar wasan kwallon kafan kasar.
Zasu gudanar da wasan sada zumunta da kungiyar wasan Three Lions ta Ingila a filin wasan Wembley a ranar 2 ga watan Yuni gabanin su halarci gasar cin kofin duniyar.
German Gernot Rohr, kociyan kungiyar wasan, zai zabo 'yan wasa 23 bayan kammala wasan sada zumuntar da zasu gudanar a ranar Asabar, wanda za'a mika sunayen ga hukumar shirya wasan kwallon kafan ta duniya a ranar Litinin.
Buhari ya bukaci Super Eagles dasu yi amfani da kuruciyarsu wajen taka rawar gani a gasar ta FIFA.
Najeriya zata fafata da Croatia, Iceland, da kuma Argentina a rukunin D. (Ahmad)