in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OIC ta bayyana goyon bayanta ga bukatar Morocco ta karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta 2026
2018-05-07 14:25:40 cri

Kungiyar hadin gwiwar kasashen musulmi OIC, ta bayyana goyon bayanta ga bukatar Morocco ta karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta shekarar 2026.

Daukacin ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ne suka amince da mara baya ga bukatar ta Morocco, yayin taronsu karo na 45 da ya gudana a Dhaka.

Shi ma taron kasashen Larabawa na 29, da ya gudana cikin watan da ya gabata a birnin Dhahran na Saudiyya, ya mara baya ga bukatar ta Morocco, inda ya bukaci dukkan kasashen Larabawa su ba Morocco dukkan goyon bayan da take bukata.

Morroco dai na neman karbar bakuncin gasar ne tare da Amurka da Mexico da kuma Canada.

Wannan ne karo na 5 da Morocco ta nemi karbar bakuncin gasar bayan ta yi rashin nasara a shekarun 1994 da 1998 da 2006 da kuma 2010. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China