An gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa a tsakanin shugabanni a fannin tattalin arziki na kasashen Asiya da tekun Pasifik karo na 19
An gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa a tsakanin shugabanni a fannin tattalin arziki na kasashen Asiya da tekun Pasifik karo na 19 a birnin Taierzhuang dake lardin Shandong na kasar Sin a ranar 4 ga wannan wata, inda shugabanni a fannin tattalin arziki da masanan bangaren zuba jari da tattara kudi, da wakilan manyan kamfanoni 500 na duniya, wadanda yawansu ya kai fiye da 300, da suka zo daga kasashe fiye da 10, ciki har da Thailand, Malaysia, Singapore da sauransu, suka maida hankali ga makomar aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku