Sin ta zama kasa ta 8 da ta mallaki tashar samar da wutar lantarki ta zafin hasken rana a duniya
A kwanakin baya, an cimma nasarar fara aikin tashar samar da wutar lantarki ta zafin hasken rana da megawatt 50 na kamfanin samar da sabbin makamashi na Delingha, wannan ce tasha ta farko ta samar da wutar lantarki ta zafin hasken rana a kasar Sin, don haka ana samun fasahohi a wannan fanni a kasar Sin, kana kasar Sin ta zama kasa ta 8 da ta mallaki tashar samar da wutar lantarki ta zafin hasken rana a duniya.
Ana iya samar da wutar lantarki ta wannan tashar a dukkan awoyi 24 na kowace rana, wanda zai kyautata samar da wutar lantarki a yankin da take shafa. (Zainab)