in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: rahoto da kasar Amurka ta gabatar dangane da kasar Sin ya sabawa gaskiya
2018-06-29 19:16:23 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya furta a yau Jumma'a cewa, wani rahoton da kasar Amurka ta gabatar mai taken "Harin da kasar Sin ta kaddamar a fannin tattalin arziki, yana barazana ga fasahohin kasar Amurka, da na sauran kasashe, gami da ikon mallakar ilimi" ya sabawa gaskiya, kana bangaren Amurka na son yin amfani da karyar da ta yi, don goyon bayan niyyarta ta daukar matakan radin kai, da kariyar ciniki.

Kakakin ya ce, matakan da kasar Amurka ta dauka sun keta ka'idojin kasuwa, sun kuma sabawa yanayin da ake ciki na samun ci gaba a duniya. Haka zalika za su yi illa ga moriyar Sin da Amurka, gami da ta kasashe daban daban.

An ce, darektan kwamitin ciniki na fadar shugabancin kasar Amurka White House, Peter Navarro ne ya sanar da wannan rahoto a kwanakin baya, wanda ya yi suka kan manufofin kasar Sin ta fuskar tattalin arziki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China