Sin: hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Turai za ta taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya
Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya furta a yau Alhamis cewa, bangarorin Sin da kungiyar tarayyar Turai ta (EU), sun cimma matsaya daya kan batutuwa da dama, tare da samar da dimbin nasarori a taron musayar ra'ayi na manyan kusoshin Sin da Turai a fannin tattalin arziki da cinikayya karo na 7, wanda aka kammala dazun nan.
A cewar kakakin, hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2, zai taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya, da bunkasa ci gabansa. (Bello Wang)