in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Amurka zai kawo ziyara Sin
2018-06-25 13:12:11 cri

Ministan tsaron kasar Amurka James Mattis zai kawo ziyara kasar Sin daga ran 26 zuwa 28 ga wannan wata, inda yayin ziyarar tasa zai gana da shugabannin kasar Sin, kuma za su tattauna kan dangantakar sojojin kasashen biyu da wasu batutuwan da suke jawo hankulansu baki daya.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Ren Guoqiang ya bayyana a nan birnin Beijing a yau cewa, bunkasa dangantakar sojojin kasashen biyu mai karko lami lafiya ya dace da muradun bangarorin biyu, kuma shi ne abin kasashen duniya suke fata.

Sin tana dora muhimmanci matuka kan raya wannan dangantaka, kuma tana fatan Amurka za ta hada kai da kasar Sin tare da cimma matsaya daya, ta yadda bangarorin biyu za su yi kokarin raya dangantakar sojojin kasashen biyu wadda za ta zama wani muhimmin mataki dake iya kawo zaman lafiya ga dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China