in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin hakkin Bil Adam zai zabi sabuwar mambarta cikin sauri don maye gurbin Amurka wanda ta fice daga kwamitin
2018-06-21 09:58:49 cri

Shugaban kwamiti mai kula da hakkin Bil Adam Vojislav Suc ya bayyana a jiya 20 ga wata a birnin Geneva cewa, kwamitin zai zabi sabuwar mambarta bisa tsari cikin sauri don maye gurbin Amurka wadda ta yi ikirarin janye jikinta daga kwamitin.

A wannan rana a gun taron kwamitin karo na 38 da aka yi a birnin Geneva, Suc ya ce, kwamitin shi ya kasance dandali daya tilo a duniya da aka iya tattauna hakkin Bil Adam tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, ko wani batun hakkin Bil Adam, inda ba za a iya tattauna karkashin kwamitin ba, sai ba za a iya warware shi ba ko ina.

Wakiliyar dinidindin ta Amurka dake MDD Nikki Haley ta sanar da ficewar kasarta daga kwamitin a ranar 19 ga wata, ta ce, kwamitin na nuna bambamcin ra'ayi kan Isra'ila kuma ba zai iya kiyaye hakkin Bil Adam yadda ya kamata ba.

Bisa bayanan da aka bayar, an ce, kwamiti na kunshe da mambobi 47, inda aka zabi Amurka ta zama mamba a babban taron MDD karo na 63 da aka yi a watan Mayun shekarar 2009. Wa'adin Amurka cikin kwamitin a wannan karo ya fara daga shekarar 2017 zuwa 2019. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China