Jerin sassan zuba jarin da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta fitar tare da hadin gwiwar ma'aikatar cinikayyar kasar, zai fara aiki ne a ranar 28 ga wata Yulin wannan shekara da muke ciki.
Bugu da kari, jarin sunayen sassan zuba jari ta ake kira, " Matakan tafiyar da mulki na musamman game da baiwa kamfanonin ketare damar zuba jari na shekarar 2018, zai maye gurbin kundin dake yiwa kamfanonin ketare jagora game da harkokin zuba jari na shekara 2017 da aka yiwa gyaran fuska.
Sabbin sassan za su kara baiwa kamfanonin ketare damar zuba jari a kanana da matsakaita da ma manyan bangarori, inda ya yi karin haske a fannoni 22 na matakan kara bude kofa da suka shafi harkokin kudi sufuri da ayyuka hidima na musamman, kayayyakin more rayuwa, makamashi da albarkatu da kuma bangaren aikin gona.
Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta ce, an rage yawan fannoni ne daga 63 zuwa 48, don kara rage amincewar da kamfanonin ketare ke samu na zuba jari a wadannan sassa. (Ibrahim)