Kamfanoni da dama sun maida kasar Sin matsayin kasa ta farko da za su zuba jari a duniya
Kungiyar cinikayya ta Amurka dake yankin kudancin kasar Sin, ta gabatar da takardar bayani kan yanayin ciniki na kasar Sin ta shekarar 2018 da kuma rahoton musamman kan halin tattalin arzikin yankin na bana, inda ta bayyana cewa, masu zuba jari na duniya sun fi son kasar Sin, kana birnin Guangzhou na kasar ya zama birni mafi karbuwa a fannin zuba jari.
Kungiyar cinikayyar wadda ta bayyana haka a jiya Alhamis, ta kuma gabatar da irin wannan takardar bayani na shekaru 10 a jere da kuma irin wannan rahoton musamman kan yanayin tattalin arziki har na tsawon shekaru 16 a jere, wadanda suka zama muhimman hanyoyi na duba makomar tattalin arzikin kasar Sin ga kamfanonin kasashen waje. (Zainab)