A cewar sabon rahoton wanda ke bayani game da makomar tattalin arzikin duniya wanda bankin ya fitar, an yi kiyasin cewa, a shekarar 2017 da ta gabata ci gaban tattalin arzikin shiyyar ya farfado zuwa kaso 2.4 cikin 100, bayan dan koma bayan da ya fuskanta na kaso 1.3 cikin 100 a shekarar 2016.
Wannan karuwa ta nuna yadda tattalin arzikin kasashen Angola da Najeriya da Afirka ta kudu suka farfado.
Koda yake ci gaban bai kai yadda ake hasashe ba, yayin da har yanzu shiyyar ke fama da rashin masu zuba jari da koma baya ta fannin kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.
Sai dai rahoton ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kaso 2.5 cikin 100 a wannan shekara. Wannan ya biyo bayan hasashen da ake kan karuwar man da ake hakowa a kasar da yadda gyare-gyaren da mahukuntan kasar ke aiwatarwa zai farfado da bangaren da ba na mai ban a kasar.
Bugu da kari, a cewar rahoton, ana saran kasashen da ba su da albarkatu za su karu cikin sauri, a hannu guda kuma sakamakon karuwar zuba jari, an yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire zai bunkasa da kaso 7.2 cikin 100 a shekarar 2018, Senegal za ta samu karuwar kaso 6.9 cikin 100, Habasha kaso 8.2, Tanzaniya kaso 6.8, sai Kenya wadda tattalin arzikinta zai karu da kaso 5.5 cikin 100 yayin da aka samu raguwar hauhawar farashin kaya.(Ibrahim)