in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce yara ne ke ci gaba da jin jiki a rikicin DRC
2018-06-27 09:40:51 cri

Wani rahoton MDD ya ce, yara ne ke ci gaba da jin jiki a rikicin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC, sannan an take hakkokinsu sama da 11,500 tsakanin shekarar 2014 da 2017.

A cewar rahoto na 6 na sakatare janar na MDD kan yara a yankunan dake fama da rikici, wanda ya mayar da hankali kan Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, adadin hakkokin da bangarori sama da 40 suka take, ya karu da kaso 60 idan aka kwatanta da na shekaru 3 da suka gabaci lokacin rahoton.

Duk da cewa rahoton ya alakanta mafi yawan masu aikata laifin da kungiyoyi masu dauke da makamai, ya ce jami'an tsaron kasar sun aikata 1 bisa 3n laifukan a tsakanin wadancan shekaru.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, jami'an tsaron kasar sun dauki matakan kawo karshe da kare horarwa da amfani da yara a matsayin sojoji.

Sai dai kuma, har yanzu kungiyoyin na ci gaba da horar da yara, yana mai cewa, adadin yaran da aka yi amfani da su a matsayin sojoji ya karu zuwa kusan kaso 50 a shekarar 2017. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China